Kasashen Turai Sun Bayyana Cewa Za Su Yi Aiki Da Hukuncin Kotun Duniya Na Sammacin Kamo Netenyahu Da Minstansa Na Yaki

Jami’in da yake kula da siyasar waje ta tarayyar turai Joseph Boris ya ce; Dole ne a girmama hukuncin da kuma aiki da shi. Kasashen

Jami’in da yake kula da siyasar waje ta tarayyar turai Joseph Boris ya ce; Dole ne a girmama hukuncin da kuma aiki da shi.

Kasashen Holand da Faransa, Canada  da kuma Ireland sun ce za su yi aiki da hukuncin da kotun kasa da kasa ta manyan laifukan ta fiyar na kamo Fira ministan HKI Benjamin Netanyahu da kuma ministansa na yaki Yoav Gallant.

A falasdinu, kungiyar Hamas ta yi maraba da wannan hukunci na samamcin kamo wadanda ta kira da ‘yan ta’adda.

Jim kadan bayan fitar da wannan hukuncin, HKI ta cigaba da yi wa Falasdinawa kisan gilla, inda a cikin sa’oi kadai ta yi kisan kiyashi har sau 5.

Amurka ce kadai ta nuna kin amincewarta da hakuncin kuton ta manyan laifuka ta kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments