Kasashe mambobin kungiyar hadin guiwa ta Shanghai, sun yi kakkausar suka ga matakan da suka hadassa bala’in jin kai a Zirin Gaza.
A sanarwar karshen taronsu na Astana, mambobin kungiyar sun yi jawabi kan jerin kalubalen da duniya ke fuskanta tare da jaddada bukatar samar da hanyar da ta dace kan batun Falasdinu.
A cewar Sputnik, kasashe mambobin kungiyar sun bayyana damuwarsu game da ci gaba da tabarbarewar rikicin Isra’ila da Falasdinu.
Yayin da suke bayyana matukar damuwarsu game da yadda rikicin Isra’ila da Falasdinu ke ci gaba da ruruwa, kasashe mambobin kungiyar sun yi kakkausar suka ga matakin da ya janyo hasarar rayukan fararen hula da dama da kuma mummunan halin jin kai a zirin Gaza.