Shugabannin kasashen musulmi da na larabawa sun bukaci Isra’ila da ta gaggauta dakatar da kazamin yakin da take yi a zirin Gaza da kuma Lebanon da ta yi wa kawanya.
Kasashen sun bayyana hakan ne a taron kolinsu na hadin gwiwa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da (OIC), a birnin Riyad na Saudiyya.
Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya yi Allah-wadai da kisan gillar da ake yi wa Falasdinawa da mutanen Lebanon.
Shi ma Ahmed Aboul Gheit, babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa, ya bi sahun yarima mai jiran gado na Saudiyya wajen yin Allah wadai da yakin da Isra’ila ke yi a Gaza da Lebanon. Inda ya ce “Kalmomi ba za su iya bayyana halin da al’ummar Falasdinu ke ciki ba.”
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi kira ga kasashen Larabawa da na Musulunci da su tsaya tsayin daka da al’ummar Falasdinu.
A nasa bangare Sarki Abdallah na biyu na Jordan ya yi Allah wadai da yakin da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma yaduwar yakin da ake yi a kasar Labanon, sannan ya yi kira da a kara kai dauki ga yankin Falasdinu da aka wa kawanya.
Shugaba Tinubu na Najeriya, a bayyanin da ya yi a gaban taron ya yi kira da a kawo karshen hare-haren Isra’ila a Gaza, inda ya yi gargadin cewa an kwashe tsawon lokaci ana wannan rikicin kuma hakan ya haifar da wahalhalun da ba za a lissafa ba.
A cikin jawabin nasa, Firayim Ministan Lebanon Najib Mikati ya yi gargadin cewa “Labanon na cikin rikicin da ba a taba ganin irinsa ba.”
Shugaban Syria Bashar al-Assad ya ce ya kamata kasashen Larabawa da na musulmi su dauki kwararan matakai kan laifukan da gwamnatin Isra’ila ke aikatawa a Gaza da Lebanon, yayin da yake cewa kalamai da jawabai ba za su iya yin wani abin da zai iya kawo karshen ta’asar Isra’ila ba.
Gabanin taron, Hamas ta yi kira da a kafa kawancen kasashen Larabawa da na Musulmi don matsawa Isra’ila da magoya bayanta lamba wajen kawo karshen cin zarafin da ake yi a Gaza da Lebanon.