Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha Sun Yi Allah Wadai Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Majalisar hadin kan kasashen yankin tekun Pasha ta yi Allah wadai da matakin Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila “Knesset” na kin amincewa da kafa kasar

Majalisar hadin kan kasashen yankin tekun Pasha ta yi Allah wadai da matakin Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila “Knesset” na kin amincewa da kafa kasar Falasdinu

Majalisar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Pasha ta yi Allah wadai da matakin Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset na kin amincewa da daftarin kudurin neman amincewa da kafa kasar Falasdinu.

Babban sakataren Majalisar hadin kan kasashen na Larabawa Jassem Muhammad Al-Budaiwi, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya yi kakkausar suka, tare da yin Allah wadai, da matakin da Majalisar Dokokin haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset ta dauka na kin amincewa da daftarin kudurin, ya kuma ce; matakin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka dauka, yana matsayin keta kudurorin kasa da kasa ne a fili, da na Majalisar Dinkin Duniya da ke da alaka da batun Falasdinu, ya kuma jaddada cewa aniyar yahudawan sahayoniyya ita ce ci gaba da tada zaune tsaye da kuma yin barazana ga zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya.

Al-Budaiwi ya yi kira ga kasashen duniya da su yi watsi da wannan hukunci na rashin adalci, wanda ke bayyana aniyar sojojin mamaya na fadada da’irar rikice-rikice da rashin son zaman lafiya da sulhu a yankin, yana jaddada kyakkyawar fatar kasashen Majalisar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Pasha kan batun Falasdinu da cikakken goyon bayansu na ganin an kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu mai cin gashin kanta a kan iyakokin da aka shata a ranar 4 ga watan Yunin shekara ta 1967 da babban birninta shi ne Gabashin Qudus, kuma Majalisarsu tana goyon bayan al’ummar Falasdinu don samun duk wasu hakkokinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments