Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Na Taron Koli A Saudiyya Kan Yakin Isra’ila A Gaza Da Lebanon

Shugabannin kasashen Larabawa da na musulmi sun isa kasar Saudiyya domin gudanar da wani taron koli da zai mayar da hankali kan yakin da Isra’ila

Shugabannin kasashen Larabawa da na musulmi sun isa kasar Saudiyya domin gudanar da wani taron koli da zai mayar da hankali kan yakin da Isra’ila ke yi a Gaza da Lebanon.

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya ce, mahalarta taron za su “tattaunawa kan yakin da Isra’ila ke yi a yankunan Falasdinawa da Lebanon, da kuma abubuwan da ke faruwa a yankin.”

Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta sanar da taron ne a karshen watan Oktoba, a lokacin taron farko na “kawancen kasa da kasa” da ke neman sasanta rikicin Isra’ila da Falasdinu.

Wannan dai na zuwa ne shekara guda bayan wani taro makamancin haka da aka yi a birnin Riyadh na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa mai hedkwata a birnin Alkahira da kuma kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta Jeddah, inda shugabannin suka yi Allah-wadai da matakin da sojojin Isra’ila suka dauka a Gaza da cewa “abin kunya ne”.

Akalla Falasdinawa 43,603 akasari yara da mata ne aka kashe tare da jikkata wasu 102,929 a yakin da Isra’ila ta fara a ranar 7 ga Oktoba, 2023 bayan wani harin ramuwar gayya na kungiyar Hamas.

Har ila yau Isra’ila ta kaddamar da farmaki ta kasa da kuma wani gagarumin farmaki ta sama kan kasar Labanon a karshen watan Satumba bayan shafe shekara guda tana musayar wuta a kan iyakar Lebanon a daidai lokacin da yakin Gaza.

Fiye da mutane 3,180 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Lebanon, mafi yawa a cikin makonni shida da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments