Kasashen Iran Da Pakistan  Sun Jaddada Bukatar Karfafa Alaka A Tsakaninsu

Fira ministan kasar Pakistan Shabaz Sharif wanda ya karbi bakuncin jakadan Iran a Islamabad, Riza Amiri Mukaddam ya yi ishara da ganawar da ya yi

Fira ministan kasar Pakistan Shabaz Sharif wanda ya karbi bakuncin jakadan Iran a Islamabad, Riza Amiri Mukaddam ya yi ishara da ganawar da ya yi da shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi a shekarar da ta gabata, ya jadda muhimmancin bunkasa alakar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.

Bangarorin biyu sun kuma tattauna wasu batutuwa da su ka shafi kasashen biyu masu makwabtaka da juna, sannan kuma batun ziyarar da ake sa ran cewa shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi zai kai Pakistan anan gaba kadan.

Har ila yau bangarorin na Iran da Pakistan sun yaba da yadda suke aiki tare a tsakaninsu a fagen siyasar kasa da kasa domin kare al’ummar Palasdinu da kokarin kawo karshen laifukan da ‘yan sahayoniya suke tafkawa a Gaza.


A wani bayani da ofishin Fira ministan kasar ta Pakistan ya fitar ya ce;  Fira minista Shabaz Sharif, yana yin jinjina akan sakon da ya samu daga shugaban kasar Iran dangane da taya shi murnar sake zabarsa da aka yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments