Kasar Yemen Ta Yi Allawadai Da Harin HKI Akan Yankin Hudaidah

Majalisar  Shawara ta Kasar Yemen ta yi Allawadai da keta hurumin kasar da HKI ta yi, ta hanyar kai hari akan tashar jiragen ruwa ta

Majalisar  Shawara ta Kasar Yemen ta yi Allawadai da keta hurumin kasar da HKI ta yi, ta hanyar kai hari akan tashar jiragen ruwa ta Hudaida.

Sanarwar ta cigaba da cewa, irin wadannan hare-haren na ‘yan sahayoniya ba za su taba sanya Yemen daina taimaka wa Falasdinawa  da kuma al’ummar Lebanon ba.

Bugu da kari, sanarwar ta majalisar shawarar Yemen ta cigaba da cewa; Kasar Yemen tana da hakkin mayar da martani akan wannan harin da HKI ta kai mata.

A gefe daya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana harin da HKI da cewa yana nuni da adawar ga bil’adama domin ya shafi cibiyoyi na fararen hula.

Ita ma kungiyar  Jihadul-Islami ta  Falasdinu ta yi tir da harin da HKI ta kai wa tashar jiragen ruwa ta Hudaida tare da bayyana shi a matsayin laifin yaki.

Bugu da kari  kungiyar Jihadul-Islami tajinjinawa al’ummar Yemen saboda jarunta da jajurcewar da suke nuna wajen fuskantar HKI don taimakawa Falasdinawa.

Da marecen jiya Lahadi ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hari akan garin Hudaida dake gabar ruwa wanda ya shafi wajen adana man fetur da kuma tashar samar da wutar lantarki.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments