Kasar Yemen Ta Jinjinawa Iran Kan Goyon Bayan Al’ummar Falasdinu Da Ake Zalunta

Shugaban Majalisar Kolin Siyasar Kasar Yemen ya tattauna da zababben shugaban kasar Iran Shugaban Majalisar Koli ta Siyasar Kasar Yemen Mahdi Al-Mashat ya tattauna ta

Shugaban Majalisar Kolin Siyasar Kasar Yemen ya tattauna da zababben shugaban kasar Iran

Shugaban Majalisar Koli ta Siyasar Kasar Yemen Mahdi Al-Mashat ya tattauna ta hanyar wayar tarho da zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian.

A yayin wannan tattaunawa, Al-Mashat ya taya shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran murnar nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar da kuma samun amincewar al’ummar Iran Al-Mashat ya dauki nasarar zaben Iran a matsayin nasara ga al’ummar Iran da kuma juyin juya halin Musulunci, yana mai bayyana burinsa na ganin an karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta bangarori daban-daban.

Al-Mashat ya mika godiyarsa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran da al’ummar Iran bisa matsayinsu na goyon baya da bayar da shawarwari ga al’ummar Falastinu da ake zalunta.

A nashi bangaren, zababben shugaban kasar Iran Masoud Pazeshkian ya bayyana godiyarsa ga shugaban Majalisar Koli ta Siyasar Jamhuriyar Yemen bisa kiran da ya yi masa da kuma taya shi murnar nasarar da ya samu a zaben kasar Iran.

Sannan ya yaba da matakin jajircewa da shugabancin Yemen da al’ummar kasar suka dauka na goyon bayan al’ummar Falastinu.Yana mai jaddada cewa: Al’ummar Yemen sun shiga wannan yaki na Gaza da dukkan karfinsu, kuma hakika al’ummar Iran da ‘yantattun mutane a duniya sun yaba da abin da kasar Yemen ta aikata a cikin wadannan yanayi masu wuyar gaske.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments