Kasar Venezuela Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Al’ummar Falasdinu

Shugaban kasar Venezuela ya yi tir da kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu a yankin Gaza, sannan kuma ya kara da cewa

Shugaban kasar Venezuela ya yi tir da kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu a yankin Gaza, sannan kuma ya kara da cewa a kowane lokaci yana tare da al’ummar Falasdinu.

Shugaban kasar ra Venezulea Nicholas Maduru, ya fada a jiya Asabar cewa: Yana da fatan ganin Falasdinawa sun fice daga cikin wannan halin maras dadi da suke ciki, sannan sun isa ga rayuwa mai nagarta.

Har ila yau shugaban kasar ta Venezuela wanda ya gabatar da taron manema labaru a birnin Caraccus, ya kara da cewa; Ko ba dade, ko bajima, gwgawarmayar Falasdinwa za ta kai ga samun nasara.

Bugu da kari, shugaban kasar ta Venezuela ya yi fatan ganin Flaasdinawan da yawansu ya kai miliyan daya da rabid a aka tarwatsa a duniya, sun sami komawa gida, sannan kuma sun sami sulhu da zaman lafiya.

Tun farko da HKI ta shelanta yaki akan al’ummar Falasdinu musamman mutanen Gaza ne dai, kasar Venezuela ta yi tir da hakan, sannan take nuna goyon bayanta ga al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments