Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta musanta da babban murya zargin Firai ministan HKI Benyamin Natayahu na taimakawa kungiyar Hamas ta yi fasakorin makamai daga kasar zuwa zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Masar na maida martanin.Ta kuma kara da cewa, Natanyahu da kuma majalisar ministocinsa ne suka kasa cimma yarjeniyar tsagaita wuta da Hamas.
Natanyahu dai yana zargi kasar Masar da taimakawa Hamsa da shigo da makamai zuwa cikin gaza ta kan iyakar kasar da ake kira Philadelfia daga kasar Masar.
A wani labarin kuma gwamnatin kasar Iraki ma ta musanta zargin firai ministan HKI na cewa gwamnatin Masarce take taimakawa Hamas da makamai daban daban.
M’aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta bayyana cewa majalisar ministocin HKI wacce take da masu tsatsauran ra’ayin dinin ne ta hana samar da zaman lafiya a Gaza saboda dagewarsu wajen ganin an yi fatali da duk yarjeniya ta samar da zaman lafiya a Gaza.