Kasar Jordan Ta Karyata Furucin ‘Yan Sahayoniyya Na Kai Hari Kan Gabar Yammacin Kogin Jordan

Ministan harkokin wajen kasar Jordan ya bayyana cewa: Duk da’awar ‘yan mamaya na kai hari kan yankunan Gabar yammacin kogin Jordan karya ce Mataimakin fira

Ministan harkokin wajen kasar Jordan ya bayyana cewa: Duk da’awar ‘yan mamaya na kai hari kan yankunan Gabar yammacin kogin Jordan karya ce

Mataimakin fira ministan kasar Jordan kuma ministan harkokin wajen kasar Ayman Safadi ya bayyana cewa: Duk abin da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi ikirari kan dalilin kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan yankunan Gabar yammacin kogin Jordan, karya ne tsagoranta.

Al-Safadi ya kara da cewa a wani sakon da ya wallafa a dandalin “X”, a yau, Lahadi, sun yi watsi da abin da ministocin mamayar nuna wariyar al’umma masu tsattsauran ra’ayi suke kirkiro na da’awar cewa, suna fuskantar hadari, don haka suke kai hare-haren kashe-kashen kan Falasdinawa da nufin raunana karfin Falasdinawa, magana ce maras tushe.

Ya ci gaba da cewa: Mamayar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa Falasdinu, da laifukan da take aikatawa kan al’ummar Falastinu, da kuma kara ruruta wutar rikici a yankin su ne mafi girman barazana ga tsaro da zaman lafiya.

Ya ce suna hada kai da abokansu domin daukar dukkan matakan da suka dace don tunkarar hare-haren wuce gonan Isra’ila da kuma dakatar da ta’addanci kan al’ummar Falastinu da kuma barazana ga tsaron yankin. Ya kara da cewa: “Za su fuskanci duk wani yunkuri na korar al’ummar Falasdinu daga cikin yankunansu da aka mamaye ko zuwa duk wani wuri da dukkan karfinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments