Iran Ta Yi Gargadin Fadadan Yakin ‘Yan Sahayoniyya A Duk Yankin Gabas Ta Tsakiya

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi gargadin fadadan yakin da yahudawan sahayoniyya suke yi da illolinsa ga duniya Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi gargadin fadadan yakin da yahudawan sahayoniyya suke yi da illolinsa ga duniya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya yi gargadin fadadar yakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take yi a Gaza da Lebanon a dukkan yankin Gabas ta Tsakiya da kuma illar da zai yi a duniya.

A jawabin da ya gabatar a wajen taron kasa da kasa na cikar kwanaki 40 da shahadar Sayyid Hasan Nasrullahi tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Gwagwarmaya ita ce hanya daya tilo ta samun adalci, ya kuma kara da jaddada cewa; Iran za ta ci gaba da kasancewa tare da Lebanon da Gaza da kuma al’ummar da ake zalunta a yankin da kuma goyon bayan haƙƙinsu na halalcin yakar mamaya da zalunci.

Araqchi ya kara da cewa; Gwamnatin yahudawan sahayoniyya tana barazana ga tsaron duniya baki daya, ba wai kawai yankin Gabas ta Tsakiya kadai ba, tana kuma aikata laifukan yaki, yana mai jaddada cewa: Kasashen duniya suna da nauyi mai yawa na tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments