Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addanci Da Aka Kai Kasar Pakistan

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da harin bam da aka kai a birnin Quetta na kasar Pakistan Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da harin bam da aka kai a birnin Quetta na kasar Pakistan

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’ei, ya yi Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai a tashar jirgin kasa da ke birnin Quetta na kasar Pakistan a safiyar yau Asabar.

Baqa’ei ya bayyana matukar alhini ga iyalan wadanda aka kashe musu ‘yan uwa da wadanda suka jikkata amma sun tsira da rayuwarsu daga wannan aika-aika, yana mai bayyana harin da mugun aiki na ta’addanci, kamar yadda ya bayyana jajen gwamnati da al’ummar Iran ga gwamnati da al’ummar kasar Pakistan babbar kawa mai makwabtaka da Iran, ya kuma jaddada cewa wadannan ayyukan ta’addanci sun sabawa dukkan ka’idoji da dokokin shari’a da haƙƙin ɗan adam da kuma jaddada cewa babu wata hujja da za a gabatar wajen kare irin wannan rashin dan Adamtaka ƙarƙashin kowane dalili.

A yau Asabar ne mutane 22 ne suka mutu sannan wasu 46 suka jikkata sakamakon fashewar wani abu da aka dasa a tashar jirgin kasa a birnin Quetta, fadar mulkin lardin Balochistan a kudu maso yammacin kasar Pakistan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments