Kanani: Siyasar Iran Ta Kyautata Alaka Da Kasashen Duniya Ba Za Ta Sauya Ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran  ya bayyana cewa, mun samu sakonni 330 na ta’aziyya daga jami’an kasa da kasa da gwamnatocin kasashen duniya kan

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran  ya bayyana cewa, mun samu sakonni 330 na ta’aziyya daga jami’an kasa da kasa da gwamnatocin kasashen duniya kan shahidan hidima, yana mai cewa: Wannan wata alama ce ta nasarar manufofin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Nasser Kanani, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a safiyar yau, 27 ga watan Mayu , a wata ganawa da manema labarai, ya yi ta’aziyyar shahadar Ayatullah Raisi, Amir Abdullahian da sauran shahidan hidima, inda ya ce: “Tun daga ranar da hatsarin ya auku, muke ci gaba da samun sakonni daban-daban daga manyan jami’ai na da suka hada da shugabannin kasashe da shugabannin gwamnatoci daga ko’in cikin fadin duniya.

Ya kara da cewa: A cikin shekaru uku da suka gabata, Shahid Raisi da Shahid Amir Abdullahian sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa alaka da kasashen yankin da ma duniya baki daya, kuma ko shakka babu wannan rawar da suka ta haifar da ci gaba da daukaka matsayin Iran a duniya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, mun samu sakonnin ta’aziyya guda 330 daga jami’ai da gwamnatocin kasashen duniya, inda ya ce: Wannan wata alama ce da ke nuna nasarar manufofin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran a a karkashin shugabancin marigayi Ayatollah Ibrahim Raisi, kamar yadda kuma manyan tawagogi sama da 60 daga kasashe daban-daban a cikin kankanin lokaci suka iso Iran domin halartar janazar Raisi.

Ya ce : Muna godiya da aiko da sako da kuma kasantuwar ministan harkokin wajen Bahrain a cikin wannan taro, kuma mun ji bayanan da sarkin Bahrain ya yi a baya-bayan nan da kuma na kasar Bahrain. Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman kulla alaka mai kyau da kasashen da ke makwabtaka da ita, kuma tana kokarin magance rashin fahimtar juna musamman a tsakanin kasashen yankin Gulf.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da hukuncin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague ta yanke dangane da tsagaita bude wuta a Gaza da kuma yadda gwamnatin sahyoniyawan tke ci gaba da yin watsi da wannan hukunci da kuma harin da ta kai kan Rafah, Kanani ya ce: A matsayinta na mai laifi, ana zargin gwamnatin sahyoniyawan da sabawa tanade-tanade na Yarjejeniyar yaƙi da kisan kiyashi, kuma  Kotun Duniya tana da dukkanin bayanai kan hakan. Kuam hakan na wakana ne duk da cewa Kotun kasa da kasa ta bayar da umarni ga Isra’ila na dakatar da yaki da kuma harin da take kaiwa kan Rafah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments