Kakakin Majalisar Dokokin Iran Na Ziyara A Beirut Domin Nuna Goyan Baya Ga Lebanon

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Baqer Qalibaf ya isa birnin Beirut domin isar da sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci da jami’ai da al’ummar

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Baqer Qalibaf ya isa birnin Beirut domin isar da sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci da jami’ai da al’ummar kasar Iran na goyan bayan gwamnatin da al’umma da kungiyoyin gwagwarmaya na Lebanon.

Qalibaf, Yayin da ya koma Tehran daga Tajikistan a ranar Juma’a, kuma ya ce zai wuce birnin Geneva, inda zai halarci taron kungiyar ‘yan majalisar kasashen Musulmi ta OIC (PUIC) da IPU.

Mohammad-Bagher Ghalibaf ya shaida wa manema labarai cewa zai yi amfani da damar domin yin magana kan kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza da Lebanon da kuma yin kira ga mambobin kungiyoyin akan su yi matsin lamba ta fuskar tattalin arziki ga gwamnatin Isra’ila don ta dakatar da kisan kiyashin da ta ke.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments