Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Laifukan yakin ‘yan sahayoniyya a Gaza bai kasa abin kunya da aka tafka a Hiroshima da Nagasaki ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya Nasir Kan’ani ya jaddada cewa: Laifuffukan yaki da kisan kiyashi da yahudawan sahayoniyya suka aikata a Zirin Gaza ta hanyar yin amfani da haramtattun makamai da gwamnatin Amurka ta ba su ba su gaza abin kunya na hare-hare da makaman nukiliya da Amurka ta kaddamar kan Hiroshima da Nagasaki a shekaru 79 da suka gabata ba.
Kakakin na ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kan’ani ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta na X cewa: Yaya babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron duniya zai dauki tutar zaman lafiya da tsaronta?!
Ya kara da cewa: Shekaru 79 da suka gabata, yayin da aka jefa bama-bamai na atomic a Hiroshima da Nagasaki wadanda suka lakume rayukan dubban daruruwan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, Amurka ta jawo wa kanta babban abin kunya ta kasancewa kasa daya tilo da ta yi amfani da makaman nukiliya a kan bil’adama. Harin bam din da aka kai a garuruwan biyu ya zama takarda mafi girma da kuma shaida na karyar ikirarin Amurkawa a fagen kare hakkin dan Adam.