Kungiyar jihadul Islami ta Falasdinu ta bayyana maganar minister harkokin wajen Jamsu Annelena Baerbock da cewa tana da matukar hatsari.
Ita dai ministar ta jamus ta bayyana cewa: Isra’ila za ta iya kashe fararen hular Gaza zaboda ta kare kanta.”
Bayanin da kungiyar ta Jihadul-Islami ta fitar ya cigaba da cewa; Wannan maganar tana halarta kai wa fararen hula hari bisa fakewa da cewa da akwai masu makamai a cikin wannan yankin.
Haka nan kuma ta yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki mataki akan wannan zancen.