Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Suka Kan Shirun Kisan Kiyashin Da Yahudawa Ke Yi A Gaza

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Kisan kare dangi da gwamnatin Isra’ila ta yi a Gaza ya tabbatar da kawo karshen tsarin duniya Jami’ar

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Kisan kare dangi da gwamnatin Isra’ila ta yi a Gaza ya tabbatar da kawo karshen tsarin duniya

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu, Francesca Albanese, ta bayyana cewa; Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na aikata munanan kisan kiyashi a Gaza tare da kashe Falasdinawa a kullum rana da cikakken goyon bayan kasashen yammacin duniya.

Albanese ta bayyana a wata hira da ta yi da tashar talabijin ta Aljazeera cewa: Kisan kare dangi babban laifi ne da ya kamata ya girgiza duniya. A cikin watannin da suka gabata, ta sha maimaita cewa a cikin da take yi cewa tabbas kisan kiyashin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi abu ne mai tsananin muni, kuma ta kasa fahimtan yadda ake barin hakan ya faru, kuma gashi yana ci gaba da faruwa har zuwa yanzu.

Jami’ar ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi tambayar cewa: “Me ake bukata don dakatar da wannan jahannamar?”, kafin ta tabbatar da cewa abin da ke faruwa a Gaza ya tabbatar da kawo karshen tsarin duniya da aka gina bayan yakin duniya na biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments