Jami’an Tsaron Turkiyya Sun Kama Wani Dan Ta’adda De Ke Shirin Kai Harin Ta’addanci A Kasar

Jami’an tsaron Turkiyya sun kama wani dan kungiyar ISIS kafin ya kai hari a birnin Istanbul na kasar Kamfanin dillancin labaran kasar Turkiyya ya bayyana

Jami’an tsaron Turkiyya sun kama wani dan kungiyar ISIS kafin ya kai hari a birnin Istanbul na kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Turkiyya ya bayyana cewa: Jami’an tsaro da suke yaki da ta’addanci a birnin Istanbul na Turkiyya sun kama wani mutum da ake zargi da kasancewa dan kungiyar IS a wani samame da jami’an tsaron suka gudanar a safiyar yau Juma’a a yankin Bagcilar.

A halin da ake ciki kuma, ministan harkokin cikin gidan kasar ta Turkiyya ya sanar da aiwatar da wani gagarumin samame na tsaro kan kungiyar wanda ya hada larduna 23 tare da kama wasu da damad aga cikin ‘yan kungiyar ta’addancin.

Kamfanin dillacin Anadolu na kasar ya ce: An kama wanda ake zargin ne a birnin Istanbul bisa bayanan sirri da ke nuni da cewa mutumin na shirin kai harin ta’addanci a birnin.

Hukumar tsaron kasar ta sanar da cewa: Dan ta’addan ya samu horo kan kera ababen fashe-fashe a kasar Siriya kuma ya shiga kasar Turkiyya ce ba bisa ka’ida ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments