Jamhuriyar Nijar Ta Sanar Da Yanke Alakar Jakadancinta Da kasar Ukraine Nan Take

Kasar Nijar ta sanar da yanke huldar jakadanci da kasar Ukraine nan take Jamhuriyar Nijar ta sanar da yanke huldar jakadanci da Ukraine cikin gaggawa,

Kasar Nijar ta sanar da yanke huldar jakadanci da kasar Ukraine nan take

Jamhuriyar Nijar ta sanar da yanke huldar jakadanci da Ukraine cikin gaggawa, bayan samun tabbacin cewa kasar Ukraine tana goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke kai wa sojojin Mali hari daga gundumar Tin- zaouatine da ke lardin Guezzam na kasar Aljeriya.

Mahukuntan Nijar sun sanar da cewa: Sun yanke shawarar yanke huldar diflomasiyya da Ukraine cikin gaggawa, a ta bakin Amadou Abdur-Rahman, kakakin gwamnatin mulkin sojan Nijar.

Kakakin gwamnatin ta Nijar ya kara da cewa: Gwamnati a Nijar ta samu labarin munanan maganganu da ba za a amince da su ba da kakakin hukumar leken asirin Ukraine ya yi, kuma jakadan Ukraine a Senegal ya goyi bayansa.

Kakainh ya ci gaba da cewa: Maganganun Ukraine suna nuna goyon bayansu ga hadin gwiwar kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke da alhakin kai harin matsorata da na dabbanci da mayakan Tin- zaouatine suka kai kan sojojin Mali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments