Kakakin gwamnatin Iran ta bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta mayar da martani idan bukatar hakan ya ta so
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatima Muhajerani ta jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta mayar da martani idan bukatar hakan ya ta so.
Mohajerani ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a yau Talata cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran har abada ba a shirye take ta gudanar da musanye muradu da maslahar kasarta da wani abu ba, don haka ya zama wajibi ta sanar da cewa; Kada a kuskura a yi wasa da Iran ta kowace hanya kan wannan bangaren, saboda abin da ya faru a harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya 2” kadan ne daga cikin karfin Iran.
Ta ci gaba da cewa: Iran a shirye take ta mayar da martani idan bukatar hakan ya ta so, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare muradun kasa ta kowace fuska, sannan kamar yadda jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce, Iran ba za ta yi gaggawar mayar da martani ba.
Tana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani a duk lokacin da ya dace, kuma a duk inda take bukata, don haka dole ne duniya ta sani cewa: Lallai Iran ba ta taba tsokanar wata kasa ba kuma ba za taba daukan matakin wuce gona da iri kan wata kasa ba, sai dai tana cikin shirin kare kanta daga duk wani wuce gona da iri.