Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Mayar Da Martani Kan Fuska Biyun Birtaniya A Yaki Da Ta’addanci

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi soka kan fuska biyu da kasar Birtaniyya ke nunawa wajen tunkarar ta’addanci Ofishin jakadancin Iran da ke birnin Landan

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi soka kan fuska biyu da kasar Birtaniyya ke nunawa wajen tunkarar ta’addanci

Ofishin jakadancin Iran da ke birnin Landan ya soki fuska biyu na gwamnatin Birtaniya wajen fuskantar ayyukan ta’addanci ta hanyar buga wani sako da ya bayyana cewa: Ta’addancin karbabbe ne a wajen gwamnatin kasar ta Birtaniya a lokacin da aka kaddamar da shi kan Iran, amma kuma abin yin Allah wadai ne a duklokacin da aka kai kan wasu kasashe na daban.

Ofishin jakadancin Iran da ke kasar Birtaniya a cikin shafin sadarwarsa na dandalin “X” ya bayyana cewa: Aiwatar da kisan gilla kan shugaban kasar Iran marigayi Muhammad Ali Raja’e da fira ministansa Muhammad Jawad Bouhunar a ranar 30 ga watan Agustan shekara ta 1981 daga gungun ‘yan ta’addan kungiyar munafukai da Mujahidinal-Khalq, wadda kasashen duniya suka dade suna daukarsu a matsayin kungiyar ta’addanci, hakan ba abin yin Allah wadai ba ne ga mahukuntan Birtaniya. Ofishin jakadancin Iran da ke Birtaniyya ya jaddada cewa: Duk da rashin canjawar wannan kungiya daga kan manufofinsu na ta’addanci, amma gwamnatin Birtaniya ta cire sunan kungiyar daga cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda da nufin yin matsin lamba kan kasar Iran, don haka abin mamaki ne yadda wasu mambobin yan Majalisar Dokokin Birtaniya suke karbar bakwancin ‘yan kungiyar ta Mujahidinal-Khalq musamman shugabar kungiyar Maryam Rajawi a duk shekara, tare da ba ta damar yin bayani a wasu fitattun jaridun kasar ta Birtaniya.      

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments