Jakadan China A Majalisar Dinkin Duniya Ya Mayar Da Martani Kan Kasashen Turai

Kasar China ta zargin kasashen yammacin duniya da yin watsi da batun mayar da Gaza a matsayin wutar Jahannama ga rayayyu Kasar China ta yi

Kasar China ta zargin kasashen yammacin duniya da yin watsi da batun mayar da Gaza a matsayin wutar Jahannama ga rayayyu

Kasar China ta yi Allah wadai da Amurka da kasashen yammacin duniya, tana mai cewa wadannan kasashe sun yi watsi da batun yadda haramtacciyar kasar Isra’ila ta mayar da Gaza jahannama ga rayayyun  Falasdinawa.

Jakadan kasar China a Majalisar Dinkin Duniya, Fu Cong, ya bayyana haka ne a yayin da yake mayar da martani ga kasashe 15 – karkashin jagorancin Amurka da Ostireliya – cewa: Amurka dakasashen yammacin Turai suna sukar hukumomin kasar China da keta hakkin bil’adama a yankunan Xinjiang da Tibet.

Wadannan jerin ƙasashen yammacin da suka haɗa da Faransa, Jamus, Biritaniya, Kanada, Denmark, Finland, Iceland, Japan, Lithuania, Netherlands, New Zealand, Norway da Swede sun zuba ido suna ganin yadda yahudawan sahayoniyya suke gudanar da kashe-kashen gilla kan Falasdinawa tare da mayar da yankunansu a matsayin Jahannamar rayayyu.

Jakadan kasar ta China ya suki kasashen yamma a matsayin masu karya kare hakkin bil’Adama, yana mai jaddada cewa: Yanayin kare hakkin bil’adama da ya kamata a kula da shi a wannan shekara shi ne halin da ake ciki a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments