Jagora : Tabbas Amurka da Isra’ila Za Su Fuskanci Martani Mai Karfi

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gargadi Amurka da Isra’ila da cewa ko shakka babu za su fuskanci muggun martani kan

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gargadi Amurka da Isra’ila da cewa ko shakka babu za su fuskanci muggun martani kan ta’asar da suke yi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa yunkurin al’ummar Iran da jagororin kasar a bayyane yake, kuma daidai yake da nufin tinkarar girman kan duniya.

“Ba wai kawai game da ramuwar gayya ba ne, aiki ne na ma’ana – tsarin da ya dace da addini, da’a da shari’a, daidai da dokokin kasa da kasa.

Al’ummar Iran da shugabannin kasar ba za su yi kasa a gwiwa ba ko yin watsi da wannan tafarki.

Dama kafin hakan Jami’an Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun yi alkawarin mayar da martani kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai kan garuruwan Ilam da Khuzestan da ke kan iyaka da Iran da kuma tsakiyar birnin Tehran a ranar 26 ga watan Oktoban da ya shude.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yayin bikin karbe ofishin jakadancin Amurka da daliban Iran suka yi a ranar 4 ga watan Nuwamban shekarar 1979, wanda aka fi sani da ranar yaki da girman kan duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments