Jagora : Fitowar Masu Kada Kuri’a Da Yawa Zai Kunyata Makiya

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran  Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; yadda mutane masu kada kuri’a za su fito da tawa a zaben

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran  Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; yadda mutane masu kada kuri’a za su fito da tawa a zaben shugaban kasar da za za yi, zai sa Iran alfahari sannan kuma ya kunyata makiya.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabin ranar Ghadir a jiya Talata ya ce;Gudanar da zabuka wata jarabawa ce da take a gaban al’ummar Iran.

A ranar Juma’a mai zuwa ne dai al’ummar ta Iran za su kada kuri’ar zaben shugaban kasa da mutane 6 suke yin takara.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya bayyana fatansa na ganin cewa zaben da za a gudanar da ranar 28 ga watan nan na Yuni ya zamarwa Iran abin alfahari ta hanyar fitowar mafi yawancin wadanda su ka cancanci kada kuri’a.

A wani sashe na jawabin jagoran ya yi suka ga wadanda suke tsammancin babu yadda za a cigaba sai ta hanyar Amurka, yana kara da cewa, ko kadan lamarin ba haka yake ba.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; Jamhuriyar musunci ta Iran ta tabbatar da cewa kasa za ta iya samun cigaba ba tare da ta dogara da baki ‘yan waje ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments