Iyalan Imam Musa al-Sadr Sun Bukaci Rasha Ta Takurawa Kasar Libya Don Gano Makomarsa

Iyalan babban malaman addini kuma wanda ya kafa kungiyar shia-Amal a kasar Lebanon sun bukaci gwamnatin kasar Rasha ta takurawa gwamnatin kasar Libya ta cika

Iyalan babban malaman addini kuma wanda ya kafa kungiyar shia-Amal a kasar Lebanon sun bukaci gwamnatin kasar Rasha ta takurawa gwamnatin kasar Libya ta cika alkawalinta na fada masu makomar Imam Musa Sa-dr da kuma abokan tafiyansa guda biyu, wadanda suka bace a kasar ta Libya tun fiye da shekaru 40 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto Sadr al-Din al-Sadr dan babban malamin yana fadar haka a lokacinda suka gana da mataimkin ministan harkokin wajen kasar Rasha Mikhail Bogdanov a birnin Mosco a jiya Alhamis 25 ga watan Yulin da muke ciki.

Sa-dr ya kara da cewa gwamnatocin kasashen Libya da suka shude da kuma ta yanzu duk sun yiwa iyalan Imam Musa Sadar alkawalin zasu bayyana makomar sa da na Sheikh Muhammad Yaqoub da Abbas Badreddine, wadanda suke tare da shi a sanda ya bace a kasar ta Libya a shekara 1978 har yanzun babu duriyarsu.

Iyalan sun bukaci gwamnatin kasar Rasha wacce suke ganin tana da dangantaka mai karfi da gwamnatin kasar Libya, da ta matsawa gwamnatin ta aikwatar da yarjeniyar shekara 2014 wacce ta bukaci gwamnatin kasar ta Libya ta bayyana sakamakon bincike dangane da makomar wannan babban malamin da kuma abokan tafiyarsa biyu.

Imam Musa Sa-dr dai ya je kasar Libya ne bisa gayyatar tsohon shugaban kasar ta Libya Mu’ammar Kizzafi, amma tun randa ya shiga kasar ya kuma gana da shugaban ba’a sake jin duriyarsa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments