Isra’ila na fuskantar sabuwar suka game da aikata laifukan yaƙi bayan an fitar da wasu sabbin bidiyoyi da ke nuna yadda dakarunta suke lalata wata ma’ajiyar ruwan sha a kudancin Gaza, tare da wasu rahotanni da suka nuna yadda sojojinta suka yi fyaɗe ga wata Bafalasɗiniya fursuna a gidan yari da ke Negev Desert.
Wani sojan Isra’ila na Runduna ta 401 da ke aiki a Rafah ya “lalata wata ma’ajiyar ruwa a makon jiya bayan ya samu umarni daga kwamandodjinsa,” a cewar wani rahoto daga jaridar Haaretz da ake wallafawa a Isra’ila.
Kazalika wani sojan ya wallafa bidiyo a shafinsa na sada zumunta da ke nuna yadda aka “tarwatsa ma’ajiyar ruwa ta Tel Sultan domin bikin Shabbat,” in ji jaridar.
A gefe guda, sojojin Isra’ila 1200 masu tsattsauran ra’ayi sun kutsa sansanin sojoji na Sde Teiman da ke saharar Negev inda ake tsare da sojoji tara saboda samunsu da laifin yin fyaɗe ga wata Bafalasɗiniya da aka yi garkuwa da ita.