A cigaba da taimakawa Falasdinawa da suke yi, ‘yan gwgawarmayar musulunci na Iran sun kai wa sansanonin HKI hari, a tuddan Gulan da Arewacin Falasdinu dake karkashin mamaya.
“Yan gwgawarmayar sun yi amfani da jirage marasa matuki wajen kai hare-haren akan” muhimman cibiyoyi na ‘yan mamaya.
“Yan gwgawarmayar na Iraqi sun sanar da cewa, sau uku suna kai hari akan muhimman cibiyoyin ‘yan sahayoniya da safiyar yau, tare da jaddada cewa za su cigaba da kai irin wadannan hare-haren saboda mayar da martani akan kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa kananan yara da tsofaffi.
Sanarwar ta kunshi cewa, an kai harin ne da makamin “Arqab” wanda sanmfurin makami mai linzami ne na “Ballistic”.
Tun da HKI ta fara kai wa Gaza hare-hare ne a shekarar da ta gabata, ‘yan gwgawarmaya a Iraki su ka shiga sahun masu taya Falasdinawa fada, ta hanayar harba makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuki.