A ranar karshe ta wasannin Olympic na daliban makarantun sakandire da ake yi a kasar Bahrain, masu wakiltar Iran sun sami lambobin zinariya 7 da kuma tagulla a bangarori daban-daban.
‘Yan wasan kokawa na Iran ne su ka lashe lambobi 7 na zinariya, azurfa daya da kuma tagulla biyu.
‘Yan wasan na Iran da su ka sami lambobin zinariya sun hada Amir Ali HAydari, Amir Muhammad Hajivand, Armin Shamshi Pur, Abul Fadal Shiry. Sai kuma Amir Sam Muhammad, da Umid Jamur.
Dukkanin wadannan ‘yan wasan kokawar sun sami galaba akan abokan karawarsu da su ka fito daga kasashe da hakan ya sa su ka sami lambobin zinariya.
Wadanda kuma su ka sami lambar yabo ya buronz kuwa sun hada Amir Husain Sururi, da Ahmad Badruddini.
Ana yin wasannin Olympic na daliban sakandire ne a kowace shekara biyu.