Mataimakin ministan aikin gona na iRan ya yi hasashen cewa a shekarar da ake ciki kasar za ta kai ga wadatuwa da Alkamar da take nomawa, ta yadda ba sai ta shigo da ita daga waje ba.
Mataimakin ministan aikin gonar na Iran Mujtaba Khayam Nikuyi, wanda shi ne sugaban bangaren nazari da bincike na ma’aikatar gonar ta Iran ya ce; A bisa hasashen da aka yi a shekarar bana a kalla za a noma alkamar da yawanta zai kai ton miliyan 13, da zai wadata kasa ta yadda ba sai ta shigo da ita daga waje ba.
Mataimakin ministan aikin gonar na Iran ya kuma ce; Kowane mutum daya a Iran yana sarrafa abinda ya kai kilogram 150 na alkama, don haka alkama tana da muhimmanci a tsarin abinci na mutanen Iran.
Wani sashe na jawabin mataimakin ministan ya kunshi cewa; Ashekarar farko ta zangon shugabancin Sayyid Ibrahim Ra’isi an sami Karin yawan alkamar da ake nomawa da ton miliyan uku, yayin da a shekara ta biyu aka sami Karin ton miliyan 6. A cikin wannan shekarar ma ana sa rana samun Karin abinda ba zai gaza ton miliyan 6 ba, ta yadda idan hakan ta faru ba za a bukaci shigo da alkama daga waje ba.
Dangane da yawan alkamar da ake amfani da ita wajen yin burodi a kasa, mataimakin ministan ya ce, ta kai ton miliyan 13 da rabi, amma kuma ana bukatuwa da wacce ake yin tsuminta.
Har ila yau a shekarar da ta gabata gwamnati ta sayi alkama daga manoma wacce yawanta ya kai ton miliyan 10 da rabi, haka nan kuma an sami karuwar wasu ton miliyan biyu da rabi da hakan ya mayar da adadin zuwa ton miliyan 13.