Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce wajibi ne bangarorin kasa da kasa musamman kwamitin sulhu na MDD su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kare zaman lafiya da tsaro a yankin gabas ta tsakiya da duniya da kuma hana aikata laifukan cin zarafin bil adama.
Pezeshkian ya yi Allah wadai da mummunan harin da gwamnatin Isra’ila ta kai kan makarantar da ‘yan gudun hijira suka fake a cikinta a gabashin zirin Gaza, wanda ya kashe fararen hula fiye da 100.
Pezeshkian ya ce, “Tare da wannan laifi, gwamnatin Sahayoniya ta sake bayyana yanayinta na gaskiya da rashin tausayi ga duniya.”
Ya kara da cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana aiwatar da wadannan ayyuka na kisan kare dangi ne tare da goyon bayan wadanda ke kiran kansu masu kare hakkin bil’adama da fafutukar tabbatar da zaman lafiya da tsagaita bude wuta, a lokaci guda tare da bayar da goyon baya mara iyaka ido rufe ga wannan gwamnatin ta zalunci.
Shugaban na Iran ya jaddada cewa, gwamnatin Tel Aviv tana aikata irin wadannan munanan laifuka ne domin kauda hankula daga rikice-rikicen cikin gida da take fama da su.
Ya nanata cewa mummunan harin kisan gilla da Isra’ila ta yi a makarantar al-Tabi’in ya bar wani “abin kunya” ga dukkanin gwamnatocin kasashen duniya.
Shugaban na Iran ya bayyana matukar goyon bayansa ga iyalan shahidai da wadanda wannan bala’i ya rutsa da su tare da mika ta’aziyyarsa ga al’ummar Palastinu masu tsayin daka da kwamandoji da mayakan gwagwarmaya.
Iran ta yi imanin cewa, ba tare da goyon bayan Amurka ba, Isra’ila ba zata iya aikata irin wadannan manyan laifukan yakin ba, wanda hakan ke tabbatar da cewa Amurka da Isra’ila tare da suke yin kisan kiyashi a kan al’ummar Gaza.