A nan Iran, tawagogin kasashen waje 70 ne ake sa ran za su halarci bikin rantsar da zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, wanda aka shirya gudanarwa da yammacin ranar Talata.
Shugabannin kasashe 10 ne za su jagoranci tawagogin kasashensu zuwa Tehran domin halartar bikin, baya ga tawagogi 15 da shugabannin majalisun dokoki, da tawagogi 16 na mataimakan shugaban kasa, da firaministoci, da tawagogi 17 karkashin jagorancin manyan sakatarorin gwamnati da jakadu.
Za a yi bikin ne da yammacin ranar Talata 30 ga watan Yuli a zauren majalisar dokokin kasar Iran da ke Tehran babban birnin kasar.
A wani labarin kuma a gobe Lahadi ne, Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran zai mika wa Masoud Pezeshkian, da takardar tabbadar da shi a mastayin sabon shugaban kasar ta Iran.
Masoud Pezeshkian, wanda Kwararen likitan zuciya ne ya yi nasara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 5 ga watan Yuli.
Ya samu kuri’u sama da miliyan 16 a kan tsohon mai shiga tsakani na nukiliyar kasar Saeed Jalili, wanda ya samu sama da miliyan 13 daga cikin sama da kuri’u miliyan 30 da aka kada.
M. Pezeshkian zai maye gurbin tsohon shugaban kasar mirigayi Ebrahim Ra’isi, wanda ya yi shahada a wani mummunan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayu da ya gabata tare da wasu mukarabansa ciki har da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir Abdolahian.