Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Iran tana maraba da kowane mataki na kawo karshen rashin hukunta ‘yan sahayoniyya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana maraba da duk wani mataki na tabbatar da adalci da kuma kawo karshen rashin hukunta ‘yan sahayoniyya da suka aikata na kisan kiyashi, laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Falastinu da sauran wurare.
A rubutun da ya yi a shafinsa na sada zumunta kan Gaza musamman kan batun fitar da sammacin kama fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da tsohon ministan yakinsa a jiya Juma’a, Baqa’i ya jaddada cewa: Aikata munanan laifuka kisan kare dan dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a Gaza, dole ne a kan kotun kasa da kasa da ke hukunta manyan laifuka ta fitar da sammacin kama manyan masu laifukan biyu, Netanyahu da Gallant. Baqa’i ya kara da cewa: Tabbas wannan hukuncin ne da ya kamata ya hada da laifin kisan kare dangi da aka yi kan Faladinawa, wanda yake a fili duniya tana gani.