Iran Tana Kokarin Samar Da Karfin Wutar Lantarki Megawatt 20,000 Ta Hanyar Makamashin Nukiya

Mataimakin shugaban Hukumar makamashin nukiliyar Iran ya ce: Tsarin dabarunsu shi ne samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 20,000 ta hanyar makamashin nukiliya Mataimakin

Mataimakin shugaban Hukumar makamashin nukiliyar Iran ya ce: Tsarin dabarunsu shi ne samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 20,000 ta hanyar makamashin nukiliya

Mataimakin shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran Mohammad Islami ya sanar da cewa: Raya masana’antar nukiliya da samar da dukkanin ci gaban da ake bukata ita ce: Yiwuwar samun damar samar da karfin makamashin nukiliya mai karfin megawatts 20,000, kuma wannan wani lamari ne na dabi’a da ke cikin tsare-tsaren kasar Iran.

A gefen taron bikin bude ayyukan hakar ma’adinai a Zaman-abad Sagand da ke lardin Yazd (a tsakiyar kasar Iran), Eslami ya ce: A yau, dangane da ayyukan hakar ma’adinan da hukumar makamashin nukiliya ta lardin Yazd ke yi, an fara wani aiki na shirin tare da sa hannun kamfanoni masu zaman kansu a ma’adinan Zaman-abad.

Ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta lashi takwabin raya masana’antar nukiliya da samun karfin samar da makamashin nukiliya mai karfin megawatts 20,000, kuma wannan lamari ne na dabi’a da kuma tsare-tsaren da aka sanya a gaba, kuma dangane da haka Iran ta fara shirye-shiryen bin diddigin lamarin domin zartarwa.

Ya ci gaba da cewa: Domin tafiya yadda ya kamata a kan hanyar samar da makamashin nukiliya a matsayin babban shiri na kasa, daya daga cikin matakan: Ya ƙunshi ayyuka masu tasowa a ɓangaren ma’adinai don ba da damar gano abubuwan da suke aiki da wannan fasahar da kuma amfani da su bayan sarrafa su a cikin tsarin makamashin nukiliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments