Kasashen na turai da su ka kunshi Birtaniya, Jamus da Faransa sun bayyana damuwarsu akan cigaban da shirin Nukiliyar Iran na zaman lafiya yake cigaba da samu, da hakan yake a matsayin maimaicin matsayin da suke nuna wa a baya.
Sanarwar hadin gwiwa da wadannan kasashen uku su ka fitar ta bayyana cewa, karuwar yawan tataccen sanadarin “Uranium da Iran take ajiye da shi, abinda damuwa ne a gare su, suna masu riya cewa ya sabawa yarjejeniyar NPT.
Wannan matsayar ta kasashen turai din guda uku, yana zuwa ne a lokacin da su ka rufe idanunsu akan HKI wacce take da makaman Nukiliya.
Iran ta yi watsi da wannan zargin na kasashen turai din uku, wanda bias yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya ( NPT) tana da hakkin daukar mataki na daban daga yarjejeniyar da aka kulla a 2015.
Amurka a karkashin shugabancin Donald Trump ta sanar da ficewa daga cikin ‘yarjejeniyar ta Nukiliya da Iran a 2018. Bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar, Iran din ta cigaba da aiki tare dukkanin sharuddan ‘yarjejeniyar na tsawon shekara daya, domin ta bayar da dama ga sauran kasashen turai su yi da nasu nauyin, sai dai hakan ba ta faru ba saboda biye wa siyasar Amurka a suke yi.