Iran Ta Yi Watsi Da Tuhume-Tuhumen Amurka Da Burtania Dangane Da Rikici Yankin Asia Ta Kudu Da Ukraine

Jakadan kasar Iran a MDD Sa’id Iravani ya musanta zarge-zargen kasar Amurka da Burtania dangane da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya da kuma

Jakadan kasar Iran a MDD Sa’id Iravani ya musanta zarge-zargen kasar Amurka da Burtania dangane da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya da kuma kasar Ukrane.

Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta ce jakadan ya rabutawa shugaban kwamitin tsaro na majalisar a wannan karon kan wannan al-amarin.

A cikin wasikar Iravani ya kara da cewa, wasikar tana maida martani ne kan korafe -korafen da kasashen Amurka da Burtaniya suga gabatar a ranar 18 ga watan Nuwamban na wannan shekara da muke ciki a gaban babban zauren MDD, inda aka tattauna dangane da abinda ya shafi yankin gabas ta tsakiya da kuma rikicin kasar Falasdinu.

A lokacin taron dai jakadan kasar Amurka ya yi Magana tare da gabatar da zargin cewa JMI ta na da hannu a cikin rikice-rikicen da suke faruwa a  kasashen yankin gabas ta tsakiya.

Sa’id Iravani ya bayyana cewa kasashen Amurkla da Burtaniya da kuma HKI sun hada kai ne don cusa kiyayyar Iran a cikin zukatan sauran kasashen duniya da kuma Sanya su su kauracewa kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments