Iran Ta Yi Tir Da Matakin Isra’ila Na Haramta Hukumar UNRWA

Iran ta yi Allah wadai da matakin Isra’ila na haramta hukmar kula da ‘yan gudun hijira Falastinawa ta Majalisar Dinkin Duniya. Jakadan Iran a Majalisar

Iran ta yi Allah wadai da matakin Isra’ila na haramta hukmar kula da ‘yan gudun hijira Falastinawa ta Majalisar Dinkin Duniya.

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya soki matakin da Isra’ila ta dauka, yana mai bayyana hakan a matsayin yunkurin hana kai kayan agajin da ake bukata a Gaza.

Amir Saeid Iravani ya ce, “Muna yin Allah wadai da dokar da Isra’ila ta fitar a baya-bayan nan kan UNRWA da ke neman hana ta ba da tallafi mai mahimmanci ga falasdinawa”.

Ya kara da cewa Gaza a cikin shekarar da ta gabata, hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta yi sun yi barnar da ba a taba gani ba a kan fararen hula a Gaza.”

“Yanzu yankin arewacin zirin Gaza yana ci gaba da fuskantar mummunan hari, musamman a yankunan da ke da yawan jama’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments