Iran Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Girmama Tsarin Demokradiyya Na Addini A Iran

Kakakin ma’aiakatr harkokin wajen kasar Iran Dr. Kan’ani ya bayyana cewa; matsayar da Amurka ta dauka akan zaben da aka gudanar a Iran ba mai

Kakakin ma’aiakatr harkokin wajen kasar Iran Dr. Kan’ani ya bayyana cewa; matsayar da Amurka ta dauka akan zaben da aka gudanar a Iran ba mai amfani ba ne, abinda nema shi ne Amurkan ta girmama tsarin deomokradiyyar addini a  Iran.

A raanr Juma’ar da ta gabata ne dai aka gudanar da zaben shugaban kasa wanda ya bai wa Ma’sud Fizishkiyan nasara akan abokin hamayyarsa Sa’id Jalili.

Shi dai Fizishkiyan ya sami kuri’u miliyam 16, da dubu dari 384, da 403.  Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ta Iran Dr. Nasir Kan’ani wanda ya gabatar manema labaru na mako-mako ya jinjinawa zaben da aka yi bayan gushewar fiye da kwanaki 50 daga shahadar shugaba Ibrahim Ra’isi. Dangane da batun rahoton sheakra-shekara da Amurkan kan fitar akan kare hakkin bil’adama, Dr. Kan’ani ya ce; Amurkan ita ce babban misali akan take hakkin  bil’adama a duniya. Har ila yau ya zargi Amurka da sauran kasashen da suke Magana akan kare hakkin dan’adam da cewa suna fakewa da wannan batu domin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments