Iran ta yi Allah-wadai da Amurka Kan sanya ta cikin zargin kisan kai

Iran ta ce ikirarin da Amurka ke yi na zama barazana ga manyan jami’an Amurka wani “abun ban dariya” da Washington ta kirkira. Sakataren Harkokin

Iran ta ce ikirarin da Amurka ke yi na zama barazana ga manyan jami’an Amurka wani “abun ban dariya” da Washington ta kirkira.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken a ranar Laraba ya ce “Amurka na matukar bibiyar barazanar da Iran ke ci gaba da yi kan wasu manyan jami’ai, ciki har da tsohon Shugaba Donald Trump, da wasu mutanen da ke yi wa gwamnati hidima.”

A cikin wata sanarwa yau Alhamis, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kan’ani ya yi watsi da zargin na Blinken a wanda ya bayyana a matsayin “wanda ya sabawa hankali, kana maras tushe.”

“A bayyane yake cewa an kirkiri irin wadannan lamura ne saboda cimma wasu manufofi na siyasa gabanin zabe a Amurka ” in ji Kan’ani.

“Kirkirar irin wadannan zarge-zargen karya a halin da ake ciki ba zai boye hannun da gwamnatin Amurka ke da shi ba a laifuka daban-daban na kasa da kasa kan Falasdinu da Lebanon.

Kan’ani ya ce ra’ayin jama’a a duk duniya ya san “gwamnatin Amurka” da jami’anta na da hannu a wannan ta’asa da Isra’ila ke aikatawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments