Iran Ta Soki Harin Isra’ila A Yemen, Tana Mai Gargadin Hakan Zai Kara Rura Wutar Rikici A Yankin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da Isra’ila ta kai kan yammacin kasar Yemen, inda ta yi gargadin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da Isra’ila ta kai kan yammacin kasar Yemen, inda ta yi gargadin cewa irin wannan ta’addancin na iya kara tsananta halin da ake ciki a yankin.

Kakakin ma’aikatar Nasser Kan’ani, ne ya bayyana hakan, sa’o’i bayan da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari kan wasu cibiyoyi a lardin Al-Hudaidah na kasar Yemen jiya Asabar.

Ya kara da cewa, wannan bala’i mai hatsarin gaske a bangaren Tel Aviv na iya haifar da tashin hankali da kuma ruruta wutar yaki a yankin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, ya bayyana cewa gwamnatin sahyoniyawa da kawarta Amurka dake mara mata baya, su ne kai tsaye suke da alhakin mummunan halin da ake ciki sakamakon ci gaba da cin zarafin al’ummar Gaza da kuma hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen.

Isra’ila dai na mai cewa ta kai hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren da Dakarun Yeman suka kai kan birnin Tel-Aviv da safiyar ranar Juma’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments