Iran Ta Soki Amurka Saboda Siyasar Matsin Lamba Mai Tsanani Akanta

Ministan harkokin waje na Iran Abbas Arakci ya wallafa a shafinsa na X ya yi tir da Siyasar matsin lamba mai tsanani ta Amurka akan

Ministan harkokin waje na Iran Abbas Arakci ya wallafa a shafinsa na X ya yi tir da Siyasar matsin lamba mai tsanani ta Amurka akan Iran, wacce a karshe za ta kai Amurka ga cin kasa mai tsanani.

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce, wannan siyasar ce ta sa Iran ta dauki matakin jajurcewa mai tsanani,musamman dangane da abinda ya shafi shirinta na Nukiliya.Abbas Arakci ya kara da cewa wannan matakin na Iran ta fito fili a cikin shirin na Nukiliya na zaman lafiya, idan aka kwatanta shi da lokacin da ya gabata da kuma bayan kakaba wa Iran takunkumai.

 Bugu da kari, ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Duk wani sabon yunkuri na sake farfado da tsohuwar siyasa matsin lamba mai tsanani akan Iran, to zai kare ne da cin kasa mai tsanani, maimakon haka abinda ya kamata ayi aiki da shi shi ne ‘ hikima mai tsanani’ wacce za ta amfani dukkanin bangarorin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments