Iran ta ce ta kuduri aniyar mayar da martani ga matakin wuce gona da iri da Isra’ila ta dauka kan kasar a baya-bayan nan, kuma ba za ta yi watsi da hakkinta a wannan bangare ba.
“Iran ba za ta yi watsi da hakkinta na mayar da martani kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba, Wannan wani hakki ne kuma wani nauyi ne na gwamnati, don haka, muna da niyya ta gaske wajen mayar da martani,”in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei a taron manema labarai na mako-mako a wannan Litinin.
Da sanyin safiyar Asabar ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hari kan wasu cibiyoyin sojin Iran, inda suka kashe jami’an soji hudu da farar hula guda.
Bangaren soji masu tsaron sararin samaniya na Iran ya ce an samu barna kadan a wasu yankuna, inda ake gudanar da bincike kan girman su da kuma martanin da ya dace da hakan.
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya fada a ranar Lahadi cewa Iran ba ta neman yaki amma za ta bayar da darasin da ya dace game da sabon matakin wuce gona da iri na Isra’ila.
Baghaei ya ce, tofin Allah tsine kan keta hurumin kasar Iran da Isra’ila ta yi, daga bangaren kasashen yankin da ma sauran kasashen duniya, ya kara tabbatar da matsaya ta kasashen duniya akan ayyukan barna da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take aikatawa.
Ya ce; Baki ya zo daya a tsakanin Kasashen yankin kan cewa, mamayar da gwamnatin Sahayoniya ta shafe shekaru 80 tana ayi a kan yankunan Falastinu ita ce babbar matsala kuma tushen rashin tsaro a yankin
Kakakin na Iran ya jaddada cewa, kasashen yankin sun dorawa magoya bayan Isra’ila alhakin hana kungiyoyin kasa da kasa, musamman ma kwamitin sulhu na MDD daukar duk wani mataki da ya dace a kan laifukan yake da keta alfarmar kasashe da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa babu wata kasa makwabciyar Iran da zata bar Isra’ila ta yi amfani da yankinta wajen kai hari a kan Iran.
Harin wuce gonad a iri na Isra’ila a kan Iran ya fuskanci martani daga bangarori daban-daban na duniya, kamar yadda ita ma Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi Allah wadai da hakan.
Ta hanyar fitar da sanarwar, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi kakkausar suka a kan wuce gona irin Isra’ila a kasar Iran.
A rahoton jaridar Sabg ta kasar Saudiyya, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a wa wasu sassan kasar Iran tare da daukar hakan a matsayin keta hurumin kasa mai cikakken ‘yanci wanda hakan karya dokokin kasa da kasa ne.
Ta hanyar fitar da wannan sanarwa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya yi Allah wadai da duk wani tashin hankali da zai haifar da karin rashin zaman lafiya a yankin tare da yin kira ga kasashen duniya da masu fada a ji da su dauki matakin rage zaman dar-dar da kawo karshen tashe tashen hankula.
Har ila yau kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta jaddada matsayar ta ta kuma bukaci da a gaggauta dakatar da hare-haren da gwamnatin yahudawan sahyoniya a zirin Gaza da yammacin kogin Jordan da kuma kasar Lebanon.
Sanarwar ta kara da cewa, abin kunya ne yadda haramtacciyar kasar Isra’ila take aikata abin da tag a dama a kan idanun al’ummomin duniya tare da cikakken goyon baya na wasu kasashe da suke bata kariya ido rufe, inda jinin al’ummar Gaza ya zama tamkar ba jinin ‘yan adam ne ake shekarwa ba, wanda kuma sanarwar ta hada wadanann laifukan yaki na Isra’ila da abin abin da ta iakata a Iran, da cewa duka laifuka ne da suka cancancin yin Allah wadai da kuma daukar matakain dakatarsu.
Bayan wannan ta’addanci, kasashe daban-daban da suka hada da Turkiyya, Masar, Saudi Arabia, Iraki, Pakistan, Malaysia, Indonesia, Switzerland, UAE, Qatar, Syria, Jordan, Oman, Aljeriya, Bangladesh, Venezuela, Bahrain, Yemen, Lebanon, Afghanistan. Maldives, Kuwait da kuma kwamitin hadin gwiwa na yankin Gulf na tekun farisa, duk sun yi Allah wadai da harin yahudawan sahyoniya kan Iran tare da daukarsa a matsayin fatali da dokoki da ka’idoji na kasa da kasa.
Masana kar harkokin siyasa da tsaro na kasa da kasa sun yi imanin cewa, tun daga lokacin da Isra’ila ta fara kaddamar day akin kisan kiyashi kan al’ummar yankin zirin Gaza, ta bayyana a fili kan cewa tinkaho da karfin soja da take yi burg ace, domin kuma ta tabbata cewa dukkanin abin da Isra’ila ke takama da tinkaho da shi, shi ne Amurka da kasashen turai, wadanda tun asali su ne suka kafa ta a cikin kasar Falastinu, wanda da ba don su ba, da tuni Isra’ila ta shiga cikin kwandon shara na tarihi.