Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya da kutsen wasu miniscocin Isra’ila a masallacin Kudus.
Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Nasser Kanaani, ya yi kakkausar suka kan matakin da ya danganta da tsokanar da wasu ministocin gwamnatin Isra’ila da wasu gungun ‘yan kama wuri zama sukayi na shiga cikin masallacin na Al-Aqsa.
Kanaani ya jaddada cewa, irin wadannan ayyuka na tunzura jama’a, wani misali ne karara na aniyar sahyoniyawan na tada zaune tsaye da tashe-tashen hankula a yankin.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana cewa, wadannan ayyuka na nuni da hakikanin gaskiyar da ba za a iya musantawa ba cewa shugabannin gwamnatin suna da nufin tsokanar al’ummar musulmin Falastinu da ma duniyar musulmi don cimma wata manufa tasu ta wuce gona da iri.
Yayin da yake jawabi ga Amurka da wasu kasashen yammacin duniya da ke goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan, Kanaani ya bukace su da su
jajirce kan gwamnatin kasar Isra’ila na ta da kawo karshen ayyukanta a zirin Gaza.