Iran Ta Kira Yi Kungiyar Kasashen Musulmi Da Ta Yi Taron Gaggawa Akan Laifukan Da HKI Take Tafkawa

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Kazem Gharibabadi ya yi kira a jiya Juma’a da a yi taron gaggawa na kungiyar kasashen musulmi domin nuna cikakken

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Kazem Gharibabadi ya yi kira a jiya Juma’a da a yi taron gaggawa na kungiyar kasashen musulmi domin nuna cikakken goyon baya ga al’ummar Falasdinu.

Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya yi ishara da kalubalen da yake a gaban duniyar musulmi, yana mai kara da cewa: Duniyar musulmi tana cikin wani yanayi mai tsanani, tana kuma fuskantar kalubale mai yawa,musamman dangane da Falasdinu.”

Har ila yau mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya ce; “Iran tana sake jaddada nuna goyon bayanta ga Falasdinawa da hakkokinsu na kafa cikakkiyar kasa a fadin Falasdinu baki daya wacce birnin Kudus zai zama babban birninta.”

Gharibabadi ya kuma kara da cewa; Al’ummar Falasdinu da suke cikin gida da kuma waje ne suke da hakkin ayyana makomarsu ta hanyar kada kuri’ar raba gardama.”

Bugu da kari, babban jami’in diplomasiyar na Iran ya ce, ta wannan hanyar za a iya shimfida zaman lafiya mai dorewa a tsakanin musulmi, kiristoci da kuma yahudawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments