Iran Ta Ce: Gwamantin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Son Shafe Falasdinawa Ne Daga Kan Doron Kasa

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana son shafe Falasdinawa ne daga kan doron kasa Dangane da harin

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana son shafe Falasdinawa ne daga kan doron kasa

Dangane da harin ta’addancin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan  makarantar Al-Ta’bi’een da ke dauke da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa a Gaza tare da kashe daruruwan Falasdinawa da ba su ji ba ba su gani ba, Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Wannan matakin bai bar wata shakka ba dangane da aniyar yahudawan sahayoniyya ta kawar da Falasdinawa daga kan doron kasa.

Ali Baqiri Kani ya rubuta a shafin sada zumunta na “X” a yammacin jiya Asabar cewa: Sabon laifin da ‘yan sahayoniyya masu aikata laifuka da suka mamaye yankunan Falasdinawa suka aiwatar na kai hari kan wata makaranta da ake amfani da ita a matsayin mafaka ga ‘yan gudun hijira da ya kai ga shahadar Falasdinawa fiye da 100 da suka hada da mata da kananan yara wadanda ba su ji ba ba su gani ba a lokacin da suke gudanar da sallar Asubah, hakan yana tabbatar da aniyar Yahudawan Sahayoniyya na kokarin shafe Falasdinawa daga kan doron kasa.

Baqiri ya kara da cewa: Samun daidaito tsakanin kasashen duniya da cikakken sharri da ‘yan sahayoniyya suke wakilta yana daidai da maraba da yaduwar barna da kuma musun dukkanin ka’idoji da dabi’u da aka sani a cikin wayewar dan Adam.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments