Makaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Barazanar da ‘yan sahayoniyya suke yi kan kasar Lebanon lamari da ke bayyana irin dabi’arsu ta dabbanci
Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri a tattaunawarsa ta hanyar wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan kan batutuwan da suka shafi alakar kasashen biyu da kuma sabbin ci gaban da suka shafi laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata kan al’ummar Falastinu.
Baqiri ya kuma yaba da halartar tawagar Turkiyya wajen taro karo na goma sha tara na ministocin harkokin wajen kasashe mambobin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Asiya da aka yi a birnin Tehran, inda ya jaddada kara yin amfani da karfin da kungiyar hadin kan tattalin arziki ta kasashe takwas masu tasowa, da kungiyar hadin kan tattalin arziki da hadin gwiwar Kungiyar hadin kan kasashen musulmi domin bunkasa manufofin kasashe masu cin gashin kansu da kuma yankin.
Baqiri ya yi ishara da irin munanan laifukan yakin da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa kan mazauna Gaza, inda ya ce: Barazanar yahudawan sahayoniyya kan kasar Labanon ci gaba ne na laifukan da wannan lalatacciyar gwamnati take yi kan mazauna Gaza tare da bayyana irin dabi’ar dabbanci nata. A bangare guda kuma, ‘yan gwagwarmayar kasar Labanon suna shirye su kalubalanci duk wata barazanar yahudawan sahayoniyya, kuma irin karfi na musamman da ‘yan gwagwarmayar Labanon suke da shi, zai yi matukar bada mamaki ga duk wani karfin hali na ‘yan mamaya.