Iran Ta Ce; Barazanar ‘Yan Sahayoniyya Ba Ta Takaita Kan Falasdinawa Ba Kawai Har Da Al’ummar Musulmi

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamaya tana barazana ne ga al’ummar Musulmi, ba Falasdinawa kadai ba Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamaya tana barazana ne ga al’ummar Musulmi, ba Falasdinawa kadai ba

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri Kani ya bayyana cewa: Abubuwan da suke faruwa sun tabbatar da cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta barazana ga al’ummar Falastinu kadai, a’a tana barazana ne ga daukacin al’ummar musulmi. Don haka wajibi ne kasashen musulmi su dauki matakin siyasa da tsauraran matakai na zahiri don tunkarar barazanar wannan haramtacciyar kasa ‘yar mamaya.

Ministan harkokin wajen Somaliya Ahmed Al-Muallem Faqi ya gana da mukaddashin ministan harkokin wajen Iran Ali Baqiri Kani, a gefen taron kwamitin zartarwa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Jeddah na Saudiyya.

A yayin wannan taron, mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi maraba da shirin gwamnatin Somaliya na shirye-shiryen maido da dangantakar dake tsakaninta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa: Suna da imanin cewa, ya kamata kasashen musulmi su karfafa alakar da ke tsakaninsu bisa moriyar masalaharsu musamman tunkarar makiyansu. Sannan babu wani shamaki da zai hana haɓaka alaka da faɗaɗa dangantaka tsakanin Iran da ƙasashen Afirka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments