Iran Ta Bukaci Kungiyar D-8 Da Ta Taka Rawar Gani Don Inganta Hadin kai

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya ce ya kamata kungiyar hadin kan tattalin arziki ta D-8 ta inganta kyakkyawar

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya ce ya kamata kungiyar hadin kan tattalin arziki ta D-8 ta inganta kyakkyawar mu’amala a tsakanin bangarori masu zaman kansu bisa hadin kai.

Bagheri Kani ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da babban sakataren kungiyar ta D-8 Isiaka Abdulqadir Imam a birnin Tehran da ke halartar taron ministocin kasashe mambobin kungiyar ta D – 8 a Tehran.

Ya ce, akwai bukatar D-8 ta taka rawar gani a fannonin tattalin arziki da kasuwanci daban-daban domin taimakawa kasashe mambobinta wajen biyan bukatunsu.

Ya kuma yi kira ga kungiyar ta da ta kara zage damtse wajen inganta hadin kai a tsakanin kasashe mambobi domin cimma muradun kungiyar da aiwatar da tsare-tsarenta.

Ya kuma yaba da taron da ministocin harkokin wajen kasashen D-8 suka gudanar a birnin Istanbul na kasar Turkiyya da aka gudanar a baya-bayan nan kan laifukan da yahudawan sahyuniya ke yi kan al’ummar Palastinu da ke Gaza.

Bagheri Kani ya ce taron ya nuna irin tsayuwar daka na kasashe mambobin D-8 da kuma irin karfin da suke da shi na taka rawa a muhimman batutuwa a duniyar musulmi da ma duniya baki daya.

A nasa bangaren, babban sakataren D-8 ya ce Iran na taka rawar gani a kungiyar da kuma ACD.

Abdulqadir Imam ya bayyana fatansa cewa taron da ke gudana a birnin Tehran zai samar da sakamako mai kyau da kuma cimma muradun kasashe mambobin kungiyar.

Ya kuma yi karin haske kan tsare-tsare kan ajandar D-8, musamman a fannin tattalin arziki da na hada-hadar kudi, ya kuma yi maraba da shirin Iran na karfafa ayyukan hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambin kungiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments