Iran Ta Bukaci  Kasashen Musulmi Su Dakile Kisan Kiyashin Gaza

Iran ta bukaci kasashen musulmi da du yi amfani da ‘dukkan hanyoyi’ don dakile kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da aikatawa a zirin

Iran ta bukaci kasashen musulmi da du yi amfani da ‘dukkan hanyoyi’ don dakile kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da aikatawa a zirin Gaza.

Ministan harkokin wajen kasar ne na rikon kwarya ya yi wannan kiran ga kasashen musulmin.

Ali Bagheri Kani, ya yi Allah wadai da irin zaluncin da gwamnatin Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da Sheikh Abdullah bin Zayed bin Sultan Al Nahyan, ministan harkokin wajen Hadaddiyar Daular Larabawa.

Bagheri Kani ya ce “Dole ne kasashen musulmi su yi amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen kawo karshen kisan kiyashin da ‘yan sahyoniyawan suke yi a Gaza, da kuma taimakawa al’ummar yankin da ake zalunta.”

A nasa bangaren, babban jami’in diflomasiyyar EAU, Ya jaddada bukatar a kai agajin jin kai cikin gaggawa zuwa Gaza, da kuma daukar kwararan matakai na dakile hare-haren da sojojin Isra’ila ke kai wa.

” Hadaddiyar Daular Larabawa tana yin iyakacin kokarinta don dakatar da yakin da kuma aike da kayan agaji ga mutanen Gaza.

Alkalumman da ma’aikatar lafiya a Gaza ta fitar sun nuna cewa dai akalla Falasdinawa 37,337 aka kashe, ciki har da 41 da aka kashe a cikin sa’o’I 24 da suka gabata duk yawancinsu mata da kananan yara, yayin da wasu 85,299 suka samu raunuka, yayin da fiye da Falasdinawa miliyan 1.7 suka rasa matsugunansu a lokacin farmakin Isra’ila kan Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments