Iran ta bayyana kudurinta na mayar da martani ga ta’addancin Isra’ila

Iran ta ce ta kuduri aniyar mayar da martani ga matakin wuce gona da iri da Isra’ila ta dauka kan kasar a baya-bayan nan, kuma

Iran ta ce ta kuduri aniyar mayar da martani ga matakin wuce gona da iri da Isra’ila ta dauka kan kasar a baya-bayan nan, kuma ba za ta yi watsi da hakkinta a wannan bangare ba.

“Iran ba za ta yi watsi da hakkinta na mayar da martani kan  gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba, Wannan wani hakki ne kuma wani nauyi ne na gwamnati, don haka, muna da niyya ta gaske wajen mayar da martani,”in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei a taron manema labarai na mako-mako a wannan Litinin.

Da sanyin safiyar Asabar ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hari kan wasu cibiyoyin sojin Iran, inda suka kashe jami’an soji hudu da farar hula guda.

Bangaren soji masu tsaron sararin samaniya na Iran ya ce an samu barna kadan a wasu yankuna, inda ake gudanar da bincike kan girman su da kuma martanin da ya dace da hakan.

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya fada a ranar Lahadi cewa Iran ba ta neman yaki amma za ta bayar da darasin da ya dace  game da sabon matakin wuce gona da iri na Isra’ila.

Baghaei ya ce, tofin Allah tsine kan keta hurumin kasar Iran da Isra’ila ta yi,  daga bangaren kasashen yankin da ma sauran kasashen duniya, ya kara tabbatar da matsaya ta kasashen duniya  akan ayyukan barna da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take aikatawa.

Ya ce; Baki ya zo daya a tsakanin Kasashen yankin kan cewa, mamayar da gwamnatin Sahayoniya ta shafe shekaru 80 tana ayi  a kan yankunan Falastinu  ita ce babbar matsala kuma tushen rashin tsaro a yankin

Kakakin na Iran ya jaddada cewa, kasashen yankin sun dorawa magoya bayan Isra’ila alhakin hana kungiyoyin kasa da kasa, musamman ma kwamitin sulhu na MDD daukar duk wani mataki da ya dace a kan laifukan yake da keta alfarmar kasashe da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa babu wata kasa makwabciyar Iran da zata bar Isra’ila ta yi amfani da yankinta wajen kai hari a kan Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments